TARIHIN JARUMI MAHESH BABU
MAHESH BABU
Sunansa Mahesh babu, ana masa lakabi da Naani, an haifeshi a 9 ga watan Agusta 1975. Shine da na hudu daga cikin biyar na 'ya'yan jarumi Krishna da Indira.Mahesh ya zauna a chennai lokacin yarintarsa tare da kakarsa Durgamma da sauran ahalin.
.
Saboda busy da mahaifinsa yake shiga ta harkar fim yasa yayansa Ramesh yake kula dashi akan lamuransa. Ya kan buga wasan Cricket a VGP Golden Beach a garin chennai. Yayi makarantar ST. Bede Anglo tareda jarumi Karthi da suke matsayin abokai, sannan ya tafi Loyola College inda yayi Digiri a fannin Bachelor of commerce.
.
A wata tattaunawa da muka yi da jarumin yace, Shi da jarumi Vijay sun kasance abokai na kusa a lokacin da suke kwaleji daya tun kafin su shigo harkar fim. Bayan ya gama karatu ya sami Mai bada Umarni L. Satyanand domin samun karin kwarewa ta fanin acting, na tsawon wata uku zuwa hudu. Yana daya daga cikin jaruman da suke buga duk wani role da aka basu.
.
A lokacin da suka je shooting fim a Austrlia shida Namrata shirodkar a nan suka fara haduwa. Bayan shekara hudu suka yanke shawarar aure. Sun yi aure 31 ga Fabrairu 2005. Kafin ayi auren an samu matsaloli da yawa saboda matarsa ta bashi shekara biyu da rabi yasa iyayensa suka ƙi amincewa, amma daga baya yar uwarsa Manjula ta fahimtar dasu suka amince.Ta dalilin prabhas baya son mace mai aiki yasa Namrata ta kammala duk wasu ayyukanta sannan ta fuskanci rayuwar aure. Bayan shekara daya da auren suka haifi dan su na farko, daga nan a shekarar 2012 suka sake haifar santaleliyar yarinya.
.
Lokacin da Mahesh yake shekara hudu ya ziyarci wurin daukar fim din Neena 1979 a nan ne aka haska shi a wasu wurare na cikin fim din.
Mahesh Babu ya kara fitowa a film yana da shekara 8 da film me Poratam a matsayin yaro ya fito a 1983
daga nan sai Shankharavam a 1987
bayan nan sai Bazaar da Mugguru kodukulu a 1988 duka dai film 8 yayi yana yaro daga 1987-1990 daga nan ya koma makaranta
.
A 1999 ne dai Mahesh babu ya dawo film a matsayin cikakken jarumin da film me suna Raja kumarudu shida jaruma Priety Zinta a 1999, fim din ya samu nasarori da daama inda a nan ne ya samu sunan Prince of Tollywood sannan ya samu kyautar Nandi Award for Best male Debut. Daga nan yayi film 2 a 2000 yuvaraju da Vamsi. Daga nan sai film din Murari a 2001, inda ya kira Murari a matsayin fim mafi muhimmaci a wurinsa sannan rawar da ya taka tana daya daga cikin wadanda yake so. Murari shima ya samu nasara har ya lashe kyautar Nandi Special Jury
.
Fina finansa guda 2 da yayi a shekarar 2002 Takkari da Bobby ba suyi wani abin kirki ba a box office. Ya saki fina finai biyu a shekarar 2003 Okkadu da Nijam, inda okkadu ya zama Highest Grossing Telugu film a wannan shekarar inda ya amshi crore 23 a box office. Ya samu kyautar Filmfare award a karon farko saboda kokarin da yayi. Shi kuma Nijam bai yi wani abin kirki ba.An jiyo Rediff.com na yabon Mahesh babu inda yake cewa mahesh ne kadai dalilin da yasa za a kalli film din Nijam. Ya samu Nandi award ta farko for Best male Actor saboda kokarinsa.
.
A 2004 yayi Naani shida jaruma Amisha Patel, fim din ya zama flop a boxoofice, faduwar Naani ce da dakushe tauraruwar mahesh da manjula wanda yasa suka dauki hutu a Goa kafin su dawo harkar fim. Daga nan sai Athadu a 2005 wanda shima ya zama highest grossing films of the year
.
Film din Pokiri ne film din sa na 2006, wanda Vijay da Salman Khan suka kwaikwaya, wanda ya samu budget na miliyan 100. Aka yi shooting nasa a tsakanin wata shida, Pokiri sai da ya zama Highest Grossing Telugu Films of all time har karshen zamaninsa sannan aka haskashi a IIFA Awards karo na bakwai a Dubai. Mahesh ya samu yabo daga Y. Sunita Chowdary ta jaridar The Hindu tana cewa "Mahesh yayi kokari da rawar da ya taka wanda ya bashi damar rike kambun matsayin Tauraro". Yayi Sainikudu duk a 2006 akan budget na kudi mai yawa amma sai ya zama flop a boxoffice.
.
Athidi ne film nasa na 2007 Wanda yake nufin Bako da Hausa shida jaruma Amrita Rao yayinda ya kasance shine fim dinta na farko, yayan Mahesh ne wato Ramesh ya shirya fim din. A shekarar 2008 ne yayi murya a wani fim mai suna Jalsa.Bayan hutu da ya dauka na wata bakwai bai kai ba ya dawo bayan wata biyu yayi film din Khaleja amma bai samu damar ci gaba da film ba saboda mutuwar kakarsa da kuma mutuwar iyayen matarsa Namrita
.
An sake ganinsa a 2011 da film me suna Dookudu wanda aka kwafi wasu sassa daga fim din Germany mai suna Good Bye, Lenin! Sai Businessness man dukansu sunyi wuta a kasuwa. Jaridar The los Angeles Times ta kira Dookudu a matsayin Biggest hit din da ba'a taba gani ba . Shima Businessman ya samu yabo daga Critics ciki har da ita Y . Sunita chowdary.
.
Bayan nan sai ya fara film din Seethamma Vikitlo Srimalle Chettu wanda shima ya zama Highest Grossing Telugu films sannan ya zama Hat-Trick ga mahesh na fina finai uku masu nasara a jere. A 2014 yayi film 2 Nenokkadine wanda ya kara samun yabo daga critics, sannan ya zama na hudu a Tarihin Highest grossing telugu films a U.S.A sai Aagadu wanda ya zama flop a box office.
.
Daga nan a 2015 an ganshi a Srimanthudu (Me arziki) daga kampaninsa wanda shi ya zama fim din kampaninsa na farko da ya shirya. Bayan wannan fim din ne wasu daga cikin Yan siyasa da manyan mutane da jarumai suka fara bunkasa kananan kauyuka a kasar india, wanda shima ya koma asalin kauyensu ya bunkasa shi.
.
Bayan nan sai Brahmostavam a 2016. A 2017 Mahesh babu yayi tafiya zuwa Tamil cinema wato kollywood in da yayi film me suna SPYDER
a 2018 ya dawo Telugu in da yayi Bharat Ane Nenu
yanzu kuma yaci gaba da film me suna Maharshi
GA JERIN JADAWALIN FINA-FINANSA
Needa
Poratam
Sankharavam
Bazaar Rowdy
Mugguru Kodukulu
Gudachari 117
Koduku Diddina Kapuram
Anna Thammudu
Bala Chandrudu
Raja Kumarudu
Yuvaraju
Vamsi
Murari
Takkari Donga
Bobby
Okkadu
Nijam
Naani
Arjun
Athadu
Pokiri
Sainikudu
Athidhi
Khaleja
Dookudu
Businessman
Seethamma Vakitlo Sirimalle Chettu
1: Nenokkadine
Aagadu
Srimanthudu
Brahmotsavam
Spyder
Bharat Ane Nenu
Maharshi
QARIN BAYANI AKAN JARUMIN
Sunansa : Mahesh Babu
Asalin Sunansa : Mahesh Ghattamaneni
Inkiya : Naani, Prince, Navataram Superstar
Sana'a : Jarumi da Mai shirya FinaFinai
Ranar Haihuwarsa : 9 ga Agusta 1975
Shekaru : 43
Wurin Haihuwa : Chennai, TamilNadu, India
Tauraron Halitta : Leo
Mahaifi : Krishna Ghattamaneni (jarumi)
Mahaifiya : Indira Devi
Yan uwa : Ramesh babu (yaya)
Naresh (dan uba)
Padmavathi (yaya mace)
Manjula (yaya mace)
Priyadarsini (kanwa)
Matarsa : Namrata Shirodkar (jarumar fim)
'Ya'yansa : Sitara (mace)
Gautam Krishna (namiji)
Addini : Hinduism
Makaranta : St. Bede's Anglo Indian Higher Secondary School, Chennai
Kwaleji : Loyola College, Chennai
Matsayin karatu : Bachelor of Commerce
Albashi : crore ashrin (20)
Net worth : dala miliyan ashirin 20
Kalar Ido : Ruwan kasa
Kalar Gashi : Baki
Tsayi : sentimita 188
inci 6
Fadin kirji : inci 40
Abincin da yafi so : Biryani da Coffee
Jarumin da yafi so : Krishna Ghattamaneni
Jarumar da yafi so : Sridevi
Deepika
Trisha
Daraktan da yafi so : Mani Ratnam
Wasan da yafi so : Cricket
Adireshi : Jubilee Hills, Hydrebad, India
Abubuwan da suke birgeshi sun hada da : Karatu, Motsa jiki da Buga wasannin bidiyo wato (video games)
Wasu daga cikin abubuwan da suka shafi Mahesh
~Mahesh baya shan taba
~Mahesh yana shan giya
~Mahesh ana masa lakabi da Yariman Tollywood
~Yawancin fina-finansa jarumi Vijay ne yake maimaicinsu
~Matarsa ta bashi shekara biyu da rabi
~Ya fara fim tun yana yaro dan shekara hudu
~Fim dinsa na farko shine fim din mahaifinsa mai suna needa
~Ya fara fitowa a matsayin babban jarumi a fim din Raja kumarudu shi da jaruma Preity Zinta
~Jarumin bollywood Amitabh Bachchan shine ya yabe shi saboda kokarinsa a fim din Pokiri wanda jarumi Salman khan yayi maimaicinsa da sunan Wanted
~Yana da kampanin shirya fim mai suna G. Mahesh Babu Entertainment Pvt. Ltd
~Saboda zaman da yayi a chennai na tsawon lokaci da yana yaro yasa baya iya karanta rubutun Telugu sosai amma ya iya fadarsa
~Ya doke manyan jarumai irinsu Srk Salman da Aamir khan a jadawalin Times of India na Most Diserable Man
~Lokacin yarintarsa iya fina-finan mahaifinsa kawai yake kallo
~ Jarumin Tamil Karthi shine abokinsa tun yarinta
~Ya sanya hannu a kampanoni da yawa a matsayin ambasadansu
~Yana da halaye kyawawa wanda hakan yasa ya zama ambasada na musamman a wani asibiti sannan da wata kungiya mai suna Heal-a-Child saboda gaskiyarsa da amanarsa.
~Yana bayar da kaso 30% daga cikin kudin da yake samu a koda yaushe
~A shekarar 2018 a watan fabrairu ya sake rattaba hannu a matsayin ambasada na kampanin Protinex.
Ya samu nasarar lashe award guda ashirin da takwas da nominations guda shida daga ciki akwai Nandi awards guda Takwas kamar
Best male debut a fim din Raja Kumarudu 1999
Best male actor a fina finai kamar Nijam, Athadu, Dookudu, Srimantuhudu
Special Jry award guda uku
Sai Filmfare award guda biyar kamar
Best male actor guda biyar a shekarar 2003, 2006, 2011, 2013 da 2015
Akwai IIFA award guda daya, sai CineMAA guda uku da sauransu.

![]() |
Jarumi Mahesh Babu tare da matarsa |
![]() |
Jarumi Mahesh Babu tare da Mahaifiyarsa |

Great work
ReplyDelete