Jadawalin Fina-Finan Prabhas

BAYAN SAAHO WANNE FIM PRABHAS ZAI YI ??

Prabhas Fans of 9ja

  Tun bayan zuwan Blockbuster Baahubali hankulan mutanen India ya koma kan Jarumi Prabhas. Yaushe Prabhas zai saki sabon fim, Yaushe Prabhas zai yi Aure sune tambayoyin da suke kai kawo a kafafen sada zumunta.
   Film din Prabhas na 20 shine film din da babu wanda ya san komai akansa. Kaso na farko na film an kammala shi yayinda kuma Rade Radi kala kala suke ta yawo akan film din. Kamar yadda majiyarmu ta samu labari film din an Lakaba mai suna da JAAN. An samu labarai akan film din iri daban daban amma masu ruwa da tsaki na film din basu ce komai ba.
    Sai daga baya mai Daukar Hoto na film din yayi Subul da baka a wata hira da akayi dashi ya tabbatar da cewar sunan film din JAAN. A halin yanzu idan Prabhas ya kammala Saaho a watan Maris zai yi tsalle ne ya fada cikin film din Jaan wanda shima za a sake shi a karshen shekarar 2019.

Comments

Popular posts from this blog

Farillai, Sunnoni da kuma Mustahabban Alwala

Jadawalin Fina-Finan Algaita

TARIHIN JARUMI MAHESH BABU