JARUMA YAZILA Littafi na Daya Part 2

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE B
***Nasiri**Bin**Muhammad***
    Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
 NA ZAUNA TARE DA ITA HAR IZUWA RANAR HAIHUARTA. Har Hukairu ya budi zaice wani abu sai nuzaira ta tari numfashinsa ta dubi humaira tace yake 'yar uwata kada ki guji mijinki saboda ni domin shima ba shi da kowa face ke, idan babu ke akusa dashi zai iya shiga mugun hali. Ina son ki bishi kutafi tare, kada kidamu dani nayi miki alkawarin komai rintsi bazan haihu ba sai agabanki." Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube humaira takara kamkame nuzaira tafashe da kuka. Haka dai ta hakura sukayi bankwana suka rabu. Tun da hukairu da humaira suka koma daji basu kara ganin mutum ba daga cikin Himsarul Aswad saboda sunyi nesa da garin kimanin tafiyar sa'a bakwai,saidai suna ganin tafiyar fatake. Wani iko na allah yanzu Hukairu da Humaira sunsami tsawon Nassey ke magana wata hudu A wannan daji inda shi dakansa yagina musu wani narkeken gida. Harda garken dabbobinsu dasuke kiwo da rumbu na ajiye kayan amfanin gona amma ko sau daya 'yamfashi. Ko 'yan sumame basu taba kawo musu hari ba. Dalili kuwa shine akwai layar sihiri da wani boka yabashi. Wadda ya binneta a tsakiyar gidansa. Duk wani mugu idan yazo gidan bazai ganshiba koda da ranane tsaka. A ranar da cikin Humaira yacika wata takwas ne laulayi yayi mata yawa har ya zamana takasa yin komai. Ka wai saita zauna. A tsakar gidan tana kallon hukairu alokacin da yake baiwa dabbobi acikin garkensu. Koda ta dan jima tana kallonsu sai idanunta suka ciko da kwalla, Hawaye ya fara zuba. Yayin da Hukairu juyo yaga halin da take ciki sai hankalinsa ya dugunzuma yabar garken da sauri yazo gareta ya tsuguna ya rike hannunta yace matata ina dalilin kukannan naki shin jikin kine yake ciwo. Kokuwa ninayi miki badaidaiba ?"Lokacinda humaira taji wannan tambayar sai ta gyada kai tace Ba wani abu bane yasa kaga ina zubar da hawaye ba face tunanin cewa abune mawuyaci na sake ganin ranar dani kaina zanyi I rin wannan aiki dakakeyi yanzu domin ina ji ajikina abune mawuyaci na rayu daga hadarin wannan ciki danake dauke dashi." Kodajin haka sai Hukairu yayi murmushi yace. Ki daina wannan tunanin naki kisani dawo wata nan bisa umarnin boka nane domin ya tabbatar min dacewa idan kika haihu acikin gari zamu rasa abinda zaki haifa kuma zamurasa duk abinda muka mallaka. Saboda a shekarar daki haihune za ayi mugun fari da cututtuka acikin garin amma mu damuke anan wannan annoba bazata shafemuba. Koda jin haka sai Humaira tayi murmushi cikin karfin hali tace "idan zancenka ya tabbata Nassey ke magana haka ina fatan "yar uwata nuzaira tazo ta haihu tare dani domin kada annobar ta shafi abinda zata haifa." Hukairu yayi ajiyar zuciya yace "nima ina fatan haKan tafaru duk da cewa nasan halin "yar uwarki macece maicika alkawari. Lailai zata zonan ta haihu tare dake cikin kowane hali. Daga wannan rana hukairu yaci gaba da kulada humaira har cikinta ya tsufa sosai harma ranar da nakudarta tazo. A wannan ranane hankalin hukairu ya dugunzuma ainun domin basu da makota bare yasamo mace wadda zata karbi aikin ungozoma. Amma dayake dama can Yasami cikakken bayani a wajen wata tsohuwar mace tunkafin subaro cikin gari sai yayi sauri ya shigar da Humaira cikin daki ya kwantar da ita akan shimfida ya shiga taimakamata. A wannan lokacine hadari yagangamo aka fara walkiya da tsawa kafin ajima ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya kuma asannane humaira tafara kwalla ihu sakamakon nakudar data zomata. Duk da cewa Humaira nacikin tsananin shan wahala duk sanda ta kwala ihu tayi shiru saita kuma kirawo sunan "yar uwarta nuzaira. Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalin Hukairu kenan domin yana tsoron cewa idan nuzaira bata zoba har bayan haihuwar Humaira zata iya shiga cikin wani mugun halin dazata zamo sanadin salwantar Hankalinta ko rayuwarta.Kwatsam ba zato ba tsammanisai hukairu yajiyo sukuwar doki a wajen gidansa kuma adai dai lokacinne kan jaririn yafito daga jikin humaira. Namfa Hukairu yarude yarasa abinda zaiyi shin zai rabu da humairane. Ya ruga waje yagano ko nu zairace tazo. Kokuwa zai tsayane har sai yaga humaira ta haihu lafiya. Yana cikin wasu wasinne yaji humaira ta damki hannunsa da kyar, tace ya kai mijina maza ka ruga izuwa.kofar gida domin ina ji ajikina 'yar uwata ce ta iso kuma na tabbata kodai ta haihu kukuma tana cikin i rin halin da nake ciki. Karka damu dani zan iya kara sa haihu wa da kaina. Cikin matukar damuwa hukairu yace menene tabbacin hakan? Humaira tace shinna taba maka karyane? Hukairu ya girgi za kai yace baki tababa kuma ina gasgata maganarki kamar yadda nake gasgaga maganar ma haifiyata marigayiya. " Koda gama maganar sai ya mike da sauri yaruga da gudu yana fita ya arba da keken doki. Kwance acikin keken dokin nuzairace kaca-kaca da jinin haihuwa gefe kuma ga jaririn data haifa ko motsi bayayi. Itama a kwai a lamun dogon suma tayi cikin razani hukairu ya ruga gareka ya dauki jaririn ya girgiza shi kuma ya kara shi akunnuwansa yaji ko numfashi bayayi. Sai tausayi yakamashi. Adai dai wannan lokacinne kuma yajiyo kukan jarirai acan dakin da ya baro humaira nantake nuzaira tabude idanunta tayi arba da gawar jaririnta data haifa kuma taga hukairu tsaye akanta. Saita fashe da kukan bakin ciki amma da ta jiyo kukan jariri adakin humaira. Sai ta fashe da dariya cikin hanzari subiyun suka ruga izuwa cikin gidan. Da shigarsu cikin dakin da humaira take kwance saisukayi arba 'yan tagwayen jariranta mata. Guda biyu suna ta tsala kuka.kuma ita humaira ta kasance cikin Koshin lafiya. Fuskarta cike da murmushi. Koda humaira taga nuzaira babu juna biyu kuma babu komai ahannunta Nassey ke magana sai ta yunkura donta mike tsaye. Nuzaira ta ruga gareta da cikin hanzari ta kwanta tace "kwanta ki huta tukunna yake yar uwata kiyi sani cewa kin zubarda jini mai yawa ajikinki. Kafin nuzaira ta rufe bakinta humaira ta tari numfashinta tace ina abinda kika haifa nuzaira ta kalli hukairu takasa cewa komai sai humaira tayi murmushi tace "yake 'yar uwata ai baki da damuwa tunda 'ya'ya biyu na haifa saiki dauki daya ki barmin daya. " Koda jin wannan batu sai nuzaira ta cika da tsananin mamaki ta dubi hukairu shima sai yayi murmushi yace "yar uwarki tayi gaskiya domin abinda ta haifa nakine koda kuwa guda dayane zan iya amincewa ta mallaka mikishi domin zakiyimishi komai kamar yadda zata yi mishi da kanta. Nuzaira tayi murmushi ta dauki daya Jaririyar ta zauna ta shayar da ita. Bayan dukkaninsu sun nutsu sai hukairu ya dubi nuzaira cikin tsananin damuwa yace yaya akai kika baro mijinki kika tahonan ba tare da yasaniba shinkin tabbatar baisa abiyo bayan kiba? Nuzaira ta gyada kai tace aidama tun kafi ranar tazo nayi kyakykyawan shiri domin na hada baki da kuyangina tuni sun tanadi wancen keken dokin danazo dashi. Acan bayan gari kuma acikin dare muka saci jiki muka sulale muka bargarin banyarda wani daga cikin masu tsaro yagammuba kuma suna dorani akan keken dokin na umarcesu dasu share sahun keken dokin don kada aga alamar komai kafinna baro gida kuwa nabarwa mijina wasikar cewa nibazan haihuba acikin garinsa acikin irin wannan lokaci nafari da annoba tun satin jiya gari ya hargitse da wadannan matsaloli. Saboda haka ninasan cewa mijina bazai biyo sawunaba idan yaga wannan wasika. Nikam na zabi na karasa. Sauran rayuwata tare da ku anan har izuwa karshen rayuwata Nassey ke magana. Sa'adda nuzaira tazo nan azancenta sai hukairu ya jawo gwauran numfashi ya ajiye sannan yace yake Nuzara kiyi sani nasan halin mijinki fiye da kowa a duniya. Tabbas sai yabiyo bayanki dan haka zamanki anan abune mai hadarin gaske. Aduniya babu abinda mijinki yakeso sama da samun magaji. Hankalinsa bazai taba kwanciya ba idan baiga abinda kika haifaba idan yazo nan ya iske cewa abin dakika haifa ya mutu. Zai iya hallakamu nida matata da dukkan abida muka haifa. Yazama dole ki dauki wannan jaririya guda daya ki tafi da ita kikoma wajen mijinki. Nayi imani cewa a halin yanzu ya baro gari yataho nemanki. Idan baki tashi kin tafi yanzu ba kin tareshi a hanya. Tabbas zai zo har nan ya riskemu abinda nake gudu ya faru sai ya faru.
====================================
Anan zamu dakata
   Amma Kafinnan nine Nasiri Bin Muhammad  nake cewa ku kasance tare dani

Comments

Popular posts from this blog

Farillai, Sunnoni da kuma Mustahabban Alwala

Jadawalin Fina-Finan Algaita

TARIHIN JARUMI MAHESH BABU