JARUMA YAZILA Littafi na Daya Part 1

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE A
***Nasiru**Bin**Tijjani***
    Marubucin ya fara da cewa:
====================================
 A WANI ZAMANI can baya mai tsawo da ya shude a kasar kisra an yi wani karamin kauye mai suna himsarul aswad ya wanzu a yammacin birnin kisra kuma shi ne gari na karshe wanda yayi iyaka da birnin rum. mutanen birnin himsarul aswad manoma ne wadanda suka sami albarkacin kasa domin agaba daya garuruwan dake kar kashin birnin kisra babu inda ake da arzikin noma kamar himsarul aswad acikin wadannan kauye akwai wani mutum da ake kira hukairu wanda asalinsa dan uwan hakimin garinne amma saboda bambancin ra'ayi da halayyarsu sai hukairu yahakura dazama tare dan uwansa hakimi yakoma daji inda yayi gidansa kusa da gonarsa yaci gabada rayuwa a wajen tare da matarsa guda daya jal wacce akekira humaira shidai hakimin kauyen himsarul aswad wanda ake kira da suna barzuk yakasance azzalumi kuma make taci mai danne hakkin talakawa kamar yadda sarkin kisra ya zamo na wannan lokaci dalilin dayasa kenan ma yadade akan mulkin yana tayin abinda yakeso zanci gaba. Hukairu da barzuk sun kasance hassan da usaini kuma suna matukar kama da junansu tamkar antsaga kara wani abin mamaki shine matansuma yan'uwan junane kuma suma hassana da usainane. Sunan matar barzuk nuzaira. Humaira da nuzaira sun shaku da juna ainun kuma har aka yimusu aure basu rabuba tunda agidadaya suke zaune lokacan da hukairu da humaira zasuyi hijira subar cikin kauyen himsarul aswad da kyar hukaira da nuzaira suka rabu domin kankame junayi suka fashe da.matsanancin kuka A wannan lokaci shima Hukairu kuka yake koda yakama. Humaira yana kokarin banbareta daga jikin yar uwarta nuzaira saita dubeshi alokacinda Fuskarta ta jike sharkaf da hawaye tace "yakai mijina saboda me zaka rabani da yar uwata alhalin tunda aka haifemu Bamu taba rabuwaba Nikam da dai ka rabamu gwara ka barnina zauna anan gidan koda kuwa zan zama baiwar sune. ". Sa 'adda hukairu yaji wannan batu saiya dada kamuwa da tausayin Humaira "yace yake matata ki sani cewa ba a sonraina zan raba ki da 'yar uwarkiba, sai domin mugayen halayen mijinta Nassey ke magana Tabbas bazan iyaci gaba da kallon irin rashin imani da yake yiwa talakawaba tunda banida IKon Hanashi. Ni a rayuwata bantaba marin wani mutumba bare ma muyi kace nace amma shi dan uwannan nawa ba a kwana ba kwai sai yasa ankewa wani hannu kokafa. Sannan yana kwacewa mutane dukiyarsu ko matansu ya maishesu bayinsu. Kituna cewa ahalin yanzu kina da ciki tsawon wata hudu yaza ayina tafi nabarki acikin wannan hali alhalin ina son nakula da lafiyarki da kaina kuma naga abin dazaki haifa. " Sa adda Hukairu yazo nan azancensa sai hukaira ta kara fashe da matsanancin kuka da kyar tayi shiru sannan tace yakai mijina kasani cewa itama 'yar uwata nuzaira a halin yanzu tana. Dauke da juna biyu tsawon watanni hudu dai dai da nawa. Ita haihuwa abuce mai hadarin gasKe. Zan iya rasa rayuwa yayin haihuwar itama zata iya zata iya rasa rayuwarta saboda haka bana son rabuwa da 'yar uwata awannan lokaci, zan so naga ranar da zata haihu. Don haka ina rokonka daka barni na zauna tare da ita har izuwa ranar haihuwarta" hmm soyayya kenan
====================================
Anan zamu dakata
   Amma Kafin nan nine Nasiri Bin Muhammad nake cewa ku kasance tare dani

Comments

Popular posts from this blog

Farillai, Sunnoni da kuma Mustahabban Alwala

Jadawalin Fina-Finan Algaita

TARIHIN JARUMI MAHESH BABU