JARUMA YAZILA Littafi na Daya Part 3

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1} 
TYPE C
***Nasiru**Bin**Tijjani***
    Marubucin ya cigaba da cewa:
===================================
 TABBAS ZAI ZO HAR NAN YA RISKEMU ABINDA NAKE GUDU YA FARU SAI YA FARU. Kodajin wannan batu sai nuzaira ta fashe da kukan bakin ciki saboda jin cewa zata sake rabuwa da yar uwarta. Cikin tsananin damuwa Humaira ta dubi hukairu tace yakai mijina shin gidan nan na dauke da sihirin mugu bai isa yagan shiba? To ai koda dan uwanka Barzuk yazo nan bazai ga gidan ba kenan. Hukairu ya gyada kai yace ai shima yanada da irin wannan sihirin nawa kuma yana da makarinsa domin tunmuna yara boka saibur yabamu shi sa'adda mai haifimmu yakaimu gurinsa. Nuzaira bamu da ishashshan lokaci dan haka dole ne ki tashi kiyi shirin gaggawa ki koma cikin gari. " Koda jin sai Nuzaira da Humaira suka fashe da kukan bakin ciki kamar bazasu dainaba nan dai hukairu da humaira suka raka nuzaira wajen keken dokinta suka bata abinci da kayan marmari. Nuzaira ta goya jaririyar da akabata ta rungume humaira suka sake fashewa da kukan bakinciki suka kamkame juna. Da kyar suka rabu har nuzaira ta sa kafarta guda cikin keken dokin saita waigo ta dubi hukairu tace. "Yakai mijin 'yar uwata shin baka tsammanin wannan farin da annoba bazai shafi wannan jaririyar da kuka baniba". Hukairu yayi murmushi yace karki damu ba abinda zaisameta kuma ina tabbatar miki nan da kwanaki kadan wannan fari da annuba zasu kau. " Nuzaira tace wana suna zan sawa ya rinyar?" Caraf humaira tace "kisamata suna YAZILA mukuma zamu sawa tamu suna DABIRA. " Nantake nuzaira ta shiga cikin keken dokinta ta kada linzamin da wakanta tayi gaba. A can birnin Himsarul Aswad kuwa lokacin.Hadari ya gangamo a ka fara walkiya da tsa warnan sai Barzuk yatafi dakin nuzaira domin ya ga halin da take ciki saboda sanin lokacin haihuwarta yayi a ko yaushe zata iya haihuwa. Da shigar Barzuk cikin haraba bangaren nuzaira saiyaga abin mamaki. Bakomai yaganiba face dukkanin kuyan ginta akwakw kwance suna ta sharar barci al halin lokacin baccinsu bayyiba. Sannan ya ji warin banju yacika gurin gaba daya. Cikin firgici Barzuk ya toshe hancinsa ya ruga izuwa cikin dakin Nuzaira dazuwa yaga dakin wayam babu Nuzaira babu alamarta. Cikin tsananin fushi ya fita daga dakin da sauri ya kwalawa Dakarunsa kira nan da nan kwa dakarun suka rugo gare shi sai ya dubesu yace "maza kuje ku shirya hawa za afita neman matata lallai anzo an saceta batare da bata lokaciba kuwa barzuk yayi gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini. Daban tsoro ya hauwani farin ingarman doki ya jagoranci dakaru dakaru dari biyu suka fice daga cikin birnin. Babban abinda yatayarwa dasu barzuk hankali shine kokadan ba suga sawon da wakaiba bare su san hanyar daya kamata subi. Koda ganin haka sai barzuk yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak, suma dakarun nasa sai suka tsaya a bayansa. Nantake barzuk ya dauko madubin tSafinsa ya shafashi da hannunsa take barzuk yagano hanyar da yakamata yabi amma bisa mamaki saiya kasa ganin hoton komai acikin madubin tsafi face hanya kawai al'amarin daya matukar bashi mamaki kenan domin asaninsa gaba daya kasar kisra in banda sarki Daksur babu wanda ya fishi karfin sihirin tsafi wanda zai iya hada kafada da shi sai dai dan uwansa Hukairu. Hukairu kuwa ya dade dayin hijira gabarin gari gaba daya to wane ha tsabibinne haka yazo har cikin garin sa ya sace masa mata. Nan dai barzuk yakada linzamin dokinsa. Yayi gaba, dakaru suka bishi abaya duu aguje sai da su barzuk suka shafe tafiyar wajen sa'a hudu sannan suka hango wani keken doki yanufo garesu aguJe cikin mamaki su barzuk suka yi tur jiya kuma suka zare maka mansu suna jiran isowar keken dokin. Tun daga nesa kadan barzuk ya shaida keken dokin yagane na matarsa ne Nuzaira dan haka sai jikinsa yayi sanyi ya maida ta kofinsa cikin kube ya sauko da gakan dokinsa ya ruga izuwa keken dokin. A gabansa keken dokin yayi turjiya yayi arba da matarshi Nuzaira rike da linzamin dawakan fuskarta cike da annuri kuma tana dauke da goyan jariri abayanta al'amarinda ya matukar bashi mamaki kenan. Cikin tsananin farin ciki ya kama nuzaira ya sauketa dagakan keken dokin ya rungumeta sannan ya karbi jaririn dake baynta ya kura mata ido yana dariyar farin ciki daga can kuma ya turbune fuskarsa ya dubi nuzaira yace "bani labarinki yake matata wanene yazo ya saceki har cikin gidana, kuma ai na kika haifi wannan tsaleliyar jaririya mai kama dani ainun haka?" Sa'adda Nuzaira taji wannan batu saitayi murmushi tace "yakai mijina kayi sani bansan meya faruba ina cikin turakata sai naji anrufe mini fuska an shaka mini banju ahanci. " Kawai sai farkawa nayi naganni a tsakiyar dokar daji kuma babu kowa a kusa dani sai wasu mutane masu shigar bakaken kaya kuma duk sun rufe fuskokinsu idanunsu kadai ake gani suna rike da muggan makamai. Adadin mutanen yakai dubu. Babban cikinsu ne kawai da Jajayen tufafi bisa jan doki koda naga wadannan mutane sai na firgita abin da jawo tasowar nakudata kenan cikin kankanin lokaci na haifi wannan jaririyar dake hannunka acikin keken doki shugaban wa dannan mutanen ya matso kusa dani yakura min ido sannan ya bushe dadariya. Yace yake matar babban abokin gabata kisani cewa kinyi babbar sa'a da yazamana cewa kina dauke da juna biyu da tuni na hallakaki amma saboda ganin kina dauke da juna biyu shiyasa muka fasa dalili kuwa aduniya bana tausayin kowa sai mace mai juna biyu. Narasa matata ne alokacin da take nakudar haihuwar dana kuma tamutu tabarmin dan, har yau har gobe ina tausayin dan saboda ba shi da uwa. Bisa wannan hujjane zan kyaleki kikoma wajen mijinki wannan karan kan kun tsallake harina amma baza ku tsallake na gababa. Koda gama fadin haka sai ya doki daya daaga cikin da wakan keken dokina take suka zabura sukayi tatafiya dani har na hangoku akan hanya wannan shine iyakar abin da zan iya tunawa ya faru gareni ya kai mijina. 
Lokacin da nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk yacika da tsananin mamaki kuma yakamu da matukar farin ciki yace tabbas babban makiyin mune sarki Raihan yaturo aka daukeki domin ya dauki fansar yar uwarsa da na kashe amma bai sami nasara ba lallai yazama wajibi naje na sanar wa sarki daksur wannan al'amarin domin mu dauki matakin gaggawa saboda nayi mamakin yadda abokin gabarmu ya shigo har cikin kasarmu ya sace min mata batare da munsaniba yake matata ki sani yau shekara goma dayin auranmu amma bamu taba samun haihuwaba sai yanzu lallai acikin farin ciki nake mara misal tuwa dan haka yanzu da ganan birnin kisra zamu wuce nanunawa sarki wannan kyakykyawar 'ya" dakika haifa mini kuma na gaya masa maganar makiyammu Sarki raihan koda gama fadin haka sai barzuk ya shiga cikin keken dokin ya zauna kusa da nuzaira sannan daya daga cikin yaransa ya hau gaban keken dokin ya fara sarrafa dawakan aka cigaba da tafiya aka nufi hanyar da ta nufi birnin sin. 
Tunda aka fara wannan tafiya zuciyar nuzaira ta fara bugawa da karfi domin ta tabbatar da cewa da zarar sun isa gaban sarki Daksar asirinta ya tonu bisa karyar data shirgawa mijinta cewa yaran sarki raihanne suka saceta domin shi sarki Daksur ka sur gumin ma tsafine wanda ka iya ganin duk abinda yafaru tun gabannin su isa fadar tasa har aka iso cikin kisra hankalin Nuzaira atashe yake bata da sukuni al'amarin dayasa barzuk ya dubeta kenan yace yake matata lafiya naga kamar kina cikin damuwa? Tunda muka fara wannan tafiya bakice uffanba kuma babu walwala da annu shuwa afuskarki koda jin haka sai nuzaira tayi murmushi tace yakai mijina kasani cewa ban taba shiga fadar sarki Daksur ba da girmanaba saboda tun ina yarinya wata rana sa'adda mahaifina ya je dani naga an sare kan wani mutun a gabana saina firgita ainun na tsandara ihu tun daga wannan rana kullun sai nayi mafarkin wannan abu ina firgita acikin barcina saida ma haifina yanaimi taimako awajen bokansa sannan na daina wannan mugun mafarki yanzu dakace zamu fadar sarki daksur sai mafarkin ya fadomin arai saboda haka nidai bana son shiga fadar sarki Daksur ka samomin masauki agari kafin mu isa fadar. Sa'adda Nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk ya bushe dadariya yace kadaki damu yake matata lallai bazanje fadar sarki batare dake. 
Kamar yadda barzuk yayi alkawari haka abin ya kasance wato da shigarsu birnin kisra sai ya kai nuzaira cikin wani kasaitaccen gida irin na sarakai wanda ke dauke da komai na jin dadin duniya harda barori da kuyangu masu hidima. Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan domin bata ga lokacin da aka biya kudin hayar gidan ba kuma da zuwansu kofar gidan ta ga masu gadin gidan sun tsube kasa sun kwashi gaisuwa har nuzaira ta bude baki zata tambaye shi batun wannan gida sai yace saboda me zakiyi mamakin mallakar wannan gida agareni ? Shin kin manta ina daya daga cikin makusan tan sarki? Nuzaira tayi murmushi ta ce bana mamakin mallakar wannan gida agareka amma ina mamakin dalilin da ya hana ka sanar dani labarinsa Barzuk yayi murmushi yace so nake na shammace kine nabaki mamaki kinga kenan zamu tare a sabon gida nuzaira tace yanzu idan katare anan birnin ya zakayi da wakilcin sarki a kauyen Himsarul Aswad? Barzuk yayi dariya yace aiba tarewa zanyi ananba kece dai zaki tare a cikin birnin nan domin na fison 'yarmu tataso da wayewa ta zama cikakkiyar 'yar birni mai wayewar kai in yaso duk karshen mako nazo nata fi daku tare ku biyun. 
Bayan barzuk ya nunawa Nuzaira bangarenta a cikin wannan gida harta shiga ciki ta kwanta tana hutawa kuyangi suka fara mata shidima sai barzuk yayi shiri ya tafi izuwa fadar sarki daksur. 
Fadace kasaitacciya wadda aka kawatata da kayan alatu iri iri tamkar aljannar duniya sarki daksur na zaune bisa wata kerarriyar kara gar mulki ta ka saita fadawa sun kewaye shi a tsakiyar fadar ga wasu tsala tsalan 'yammata sai tikar rawa suke cikin mummunar shiga mai baiyana tsaraicinsu. 
A kaida duk sa'adda sarki ke kallon wadannan 'yammata yayin da suke tikar rawa yana dariya da murmushi amma a yau sai sarki ya turbune fuska babu annuri atare da shi ko kadan kuma tun da ya fito fadar haka ya ka sance cikin rahin walwala da sukuni kallo daya mutum zai masa yasan yana cikin tsananin bacin rai. 
Al amarin daya matukar dugun zuma hankalin fadawa kenan domin sun sancewa fushin sarki ba karamin tashin hankali bane agaresu gaba daya. Ana cikin wannan haline akaga hakimi barzuk ya shigo fadar cikin farinciki kamar wanda aka yiwa albishir din mulkin duniya cikin sauri har da hardewa barzuk ya isa gaban sarki Daksur ya zube kasa ya kwashi gaisuwa ya dago kai domin yayiwa sarki bayanin abin farin cikin da ya sameshi sai sarki yayi farat ya tashi tsaye kawai sai ya dubi barzuk yace kabiyoni izuwa cikin dakin gani ina son magana dakai a sirrance. Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yanu fi dakin gani nanfa Barzuk ya bishi da sauri aka bar fadawa da jama'ar gari a zazzaune sun yi tsurutsuru da idanuwansu suna mamakin abin da ke faruwa. Yayin da sarki Daksur da Barzuk suka shiga dakin gani sai sarki ya tsaya a tsaye maimakon ya zauna ya juyo suka fuskanci juna shida Barzuk yace kazone kayi mini aibishir bisa cewa matarka ta haifi "ya" mace koba hakaba? Cikin muryar rawar murya burzak yace hakane ya shugabana Daksur yace tokasani kasani wannan "ya" data haifa ba "yar ka bace "yar" dan uwanka ce Hukairu amma ita matarka "da" na miji ta haifa kuma a mace yazo duniya hakika matarka ta yaudareka kuma karya ta shiryama domin ka jaddada magana ta yanzu zan nuna maka duk abubuwan da suka faru azahiri. Kagani da idanuwanka. Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki yayi nuni da hannunsa izuwa ga jikin bango take hoton al'amarin suka rinka gudana tun lokacin da Nuzaira tayiwa 'yar uwarta Humaira alkawarin cewa lallai awajenta zata haihu har lokacin da aka bata jariri yarnan koda ganin wannan al'amari sai barzuk ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki jikinsa gaba daya ya kama tsuma ka wai sai ya zare ta kofi ya juya da nufin yaje ya sare kan Nuzaira amma sai sarki daksur ya daka masa tsawa ya tsaya cak ya juya ya durkusa bisa guiwowinsa a gaban sarki daksur ya mayar ka takofinsa bisa kubenta ya sunkuyar da kansa kasa alokacin da hawayen takaici yake zubo masa yace ya shugabana yanzu me ya kamata nayi? Sarki daksur yayi ajiyar numfashi sannan yace ya kai Barzuk kayi sani bisa bin ciken da nayi idan muka ka bar matarka da wannan "ya da aka bata wannan fari da annoba da muke fama dasu a gari zasu kare nan da sati biyu kacal gari zaiyi lafiya amma inda masifar take shine wannan jaririyar da matarka ta zo da ita idan har ta girma zama gawurtacciyar jaruma kuma mayakiya fiye da sarkin yakinmu sadauki Hauzar bin Mausus duk yakin da muka taro sai ta sami nasara amma fa duk sanda ta san sirrin tsafina mun banu mun lalace sai mulkimmu ya rushe. Kuma sai talakawanmu sun zama shugabanninmu sun dauki fansar zaluncin da muka dade muna yi musu tsawan shekara da shekaru ta han ya daya ce ka dai zamubi kada azo da ita fadata kada abari tayi arba da fuskata kuma kada ka nunawa matarka bacin ranka koka gaya mata abin da muka tattauna anan yanzu.
====================================
Anan zamu dakata
   Amma Kafinnan nine Nasiri Bin Muhammad nake cewa ku kasance tare dani

Comments

Popular posts from this blog

Farillai, Sunnoni da kuma Mustahabban Alwala

Jadawalin Fina-Finan Algaita

TARIHIN JARUMI MAHESH BABU