YADDA AKE SAUKE BIDIYO DAGA FACEBOOK IZUWA WAYAR ANDROID BA TARE DA WANI APPLICATION BA
YADDA AKE SAUKE BIDIYO DAGA FACEBOOK IZUWA WAYAR ANDROID
Assalamu Alaikum maziyartan wannan shafi mai Albarka, a darasinmu na yau muna dauke da yadda zaku sauke (download) na facebook izuwa wayoyinku na Android.
Kamar yadda muka sani wannan ya kasance daya daga cikin abunda ke ciwa yawancin mutanenmu tuwo a Qwarya, shine na yanke shawarar fayyace da kuma bayyana muku yadda zaku rinQa sauke Bidiyo na facebook izuwa wayoyinku na Android a hanya mafi sauQi.
Abubuwan da ake buQata
1. Opera Mini (Latest Version)
2. Data (MB) isasshiya mai Inganci
3. Facebook Account
Kamar yadda kuka gani a sama a abubuwan da muke BuQata yayin wannan aiki akwai wani bayani da nake so na muku.
~ Ita Opera Mini idan zaku dauko ta ya kasance Latest Version ce wato sabuwa ce ba Tsohuwa ba, idan kuma tsohuwar ce da kai toh sai ka shiga Play Store kayi Updating nata, domin indai ba sabuwar ba, yi da tsohuwar zai iya bada matsala.
~ Sannan kuma ya kasance Datar (MB) da zakuyi amfani da ita ta kasance mai kyau ce wacce zata iya bude muku komai, ba wacce take iya abu guda daya ba.
GA YADDA ZAKUYI
• Da farko abunda zaku yi shine ku shiga Opera Mini. Bayan kun shiga sai ku je wajen searching da aka tanade shi a sama, sai ku danna www.facebook.com
• Bayan kun danna zai fara loading yana gama loading zai kawo maku inda zaku saka bayananku na facebook,
sai ku saka lambar wayarku ko adireshin e-mail, sannan kuma ku saka lambar sirrinku (password). Sannan ku danna Log in.
• Kuna dannawa zai fara loading yana gamawa zai watso muku Facebook dinku, inda zaku ga duk wasu bayananku na facebook din.
• A nan ne sai ku nemo bidiyon da kuke son daukowa, kuna nemo shi sai kuyi maza ku danna kan bidiyon, wato ku danna inda bidiyon yake.
• Kuna dannawa zai fara loading sai kuma ya watso muku cewar shin Kallo (Play) kuke son yi ko kuma Saukewa (Download) za kuyi izuwa wayoyinku. Kamar yadda kuka gani a hoton nan na Qasa. Sai ku danna Saukewar (Download)
• Anan take zai fara downloading, yana gamawa shikenan ya sauka izuwa wayoyinku.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Mun gode da ziyartar wannan shafin namu, Da fatan zaku yaďa (share) izuwa abokanku da yan uwanku.

Kai amma naji dadi sosai
ReplyDelete