JARUMA YAZILA Littafi na Daya Part 4

***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE D
**Nasiru**Muhammad**Tijjani***
    Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
A can daji kuwa inda manomi hukairu yayi gidansa sun wayi garine a cikin farin ciki da bakin ciki dalili farincinsu shine na haihuwa da humaira tayi nayaya tagwaye mata duk da cewa tayi kyautar bayar guda ga 'yar uwarta nuzaira shi kuwa mummuna mafarkin wanda himaira tayi a jiya da daddare da safe sa adda humaira ta farka daga bacci ta fara bawa mijinta hukairu labarin mafarkinda tayi a jiya al amari daya matukar dugunzuma humaira duk hankalinsa kenan dalili kuwa shine a iya saninsa da matarsa humaira duk abin datayi mafarkinsa saiya tabbata a gaske. Bawani abu humaira ta ganiba acikin mafarki ba face saukar wadansu dakaru kamar daga sama wadanda suka bukawa gidan wuta ya kone kurmus babu abin da ya tsira. Lokacin da hukairu yaji labarin mafarkin da humaira tayi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun rasa abin dake masa dadiya shiga tunani mai zurfi daga can saiya dubi ita humaira yace yake matata kinsani cewa wajibine a garemu muyi hijra mubar gabadaya yankin wannan kasa tamu idan har muna son mu da abin damuka haifa mutsirada rayuwarmu naji ajikina cewa sarki daksar kasurgumin matsafine don haka na tabbatar da cewa abinda ya faru tsaka nimmu da 'yar uwarki nuzaira ya gani kuma ya nunawa barzuk bisa wannan da lilinne za su turo a hallakamu lokaci yayi da zan gaya miki wani sirri wanda bantaba gaya mikiba. Tun muna yara nida dan uwana barzuk bokan ma haifina wanda muka sami sirrikan tsafi a wajensa yace mana cewa agaba daya kasar nan babu wani mahaluki mai karfin sihirinmu face sarki daksar amma duk 'yar da muka haifa idan tayi arba da idan sarki daksar to zata samu duk irin sihirin da sarki daksar yake da shi a cikin kwana uku harta samu nasarar Hallaka shi ta hau kan karagarsa face ya kasheta kafin cikar kwana uku shi kansa sarki daksar ya san da wannan sirri don haka bazai taba barin abun da muka haifa arayeba dun haka ba zai barmuba yazama wajibi muyi shirin gaggawa yanzu muyi hijira mukara gaba. Sa adda hukairu yazo nan azancensa sai humaira ta ce yanzu ina kake tsammanin zamu shiga mu buya ba tare da sarki daksar yaturo an kashemuba Hukairu yace waje daya ne zamu iya zuwa muyi rayu wa acan kuma mu tsira daga sharrin sarki daksar da dan uwana Barzuk. Bawani waje bane face birnin misra inda sarki Raiyan ke mulki. " Koda jin haka sai idanun Humaira suka zazzaro tace "ya ya za ayi muje birnin misra kuma muyi rayuwa alhalin mutanen can sun kasance musulmai mukuma ma abota tsafine da gunki?
Humaira tace "shin ka manta ne sarki daksur bashi da wani makiyi wan da yafi sarki Raiyan na birnin misra? Ai idan sarki raiyan ya fashinci cewa mu mutanen birnin kisra ne sai yasa anyi mana kisan gilla domin ya dauki fansar ran 'yar uwarsa gimbiya Numaira wacce sarki daksur ya ka she yayin da aka fafata kazamin yaki da su a shekaru uku baya. " 
Hukairu yayi ajiyar numfashi sannan yace "duk nasan da wannan al'amari amma abinda nake so ki fahimta shi ne abinda ya koro bera yafada cikin wuta ya fi wutar zafi. " Koda gama fadin haka sai hukairu ya mike tsaye yakama hada kayyayyakinsu domin suyi hijira. Bayan ya gama hada hada komai a waje guda ya dora a kan rakumansa wasu kuma akan shanunsa sai yaje tsakiyar filin gidan ya haka rami sai ga shi ya tuno wata laya. Nan take ya rataya layar a wuyansa, sannan yakira Humaira ta fito da ga cikin daki goye da jaririyarta. Ba tare da bata lokaciba suka hau kan rakumansu biyu sukayi gaba suna janye dabbobinsu. Koda hukairu ya juya ya dubi gonarsa da wannan gida nasa sai idanunsa suka cikoda kwalla saboda takaicin ya tafiya bar kasa mai albarkar noma wadda abu ne mawuyaci ya sake samun irinta. 
Bayan kamar sa a hudu da tafiyar hukairu da matarsa humaira sai ga sarkin yaki haizar bin mausus bisa doki tare da dakaru dari biyar suna take masa baya dukkaninsa dauke da muggan makaman yaki tun daga nesa haizar ya dauko wani gilashi na sihiri wanda sarki daksur ya bashi ya ce da shi da wannan gilashi ne kadai zai iya hango gidan hukairu. Haizur yasa gilashin a kan idanunsa amma bai hango komaiba dan haka sai suka kara kaimin gudu bisa da wakansu. Jim kadan da faruwar haka sai suka hango gidan daga can nesa. Daya daga cikin daka runnasane ma ya fara hangowa ya nuna masa al'amarin daya matukar ba shi.mamaki kuma yaba shi tsoro ya fara tunanin duk yadda a kayi su Hukairu basa gidan kuma lallai ya tone wannan laya wacce sarki daksur ya bashi labarin cewa hukairu ya binneta a tsakiyar gidansa. Tun da ga inda suka hango gidan Haizar yabada umarnin a fara harba kibiyar wuta izuwa gidan. Ai kuwa cikin kan kanin lokaci gidan gaba daya ya kama ya kama da wuta yana ci balbal. Su sarkin yaki haizar suka karqso gaban gidan aguje bisa dawakansu suka yiwa gidan kawanya kuma suka dana kwari bisa baka suna jira suga wani abu mairai yayi fitar burgu don ceton ransa su harbeshi amma hargidan yagama konewa kurmus yazama toka ko kyanwa basu ganiba. A sannanne sarkin yaki haizar ya sakko daga dokinsa ya duba tsakiyar gidan nan take kuwa yayi arba da wannan rami wanda hukairu tone ya cire layarsa ta sihiri. Cikin tsananin ta kaici da fushi haizar ya kwarara ihu sannan ya dakko mudubin tsafinsa ya shafeshi sau uku yana mai karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku. Faruwar hakan keda wuya sai ga fuskar sarki daksur ta bayyana akan madubin suka dubi juna. Kafin haizar ya budi baki yace wani abu sai sarki daksur ya tari numfashinsa yace "maza ku ruga gaba domin tuni Hukairu da matarsa sunyi nisa, taza rarku da su ta kai nisan sa'a hudu. Idan kuka yi sakaci suka shiga yankin kasar misra shi ke nan baza ku taba riskar suba. Tun da hukairu na tare da wannan laya baza ku taba ganin koda sawunsuba amma i dan kayi amfani da wannan gilashin sihiri da na baka zaka i yaganin sawayensu. Idan har kana son kariskesu sai kunyi ta fiyar kwana uku bayada zango babu barci. Idan har kasami nasarar cika wannan aiki kana dawo wa birnin kisra zanbaka wazircina kuma zanbaka dukiya ninkin goman abin da ka mallaka a yanzu. Koda gama wannan jawabi sai fuskar sarki daksur ta bace bat, daga cikin madubin sarkin yaki haizar nan take yaji farin ciki ya lullubeshi dan haka sai yaruga kan dokinsa yayi tsalle ya haye kan dokin ya zabure shi cikin matsanancin gudu koda ganin haka sai suma ragowar dakarun suka sakarwa dawakansu linzami suka rufa masa baya. 
Tun dasu sarkin yaki haizar suka cigaba da wannan tafiya basu tsaya ba har rana ta fadi, gari yasoma duhu. A wannan lokacinne yunwa da kishirwa ta suka fara addabarsu. Sai da ta kai suna ta fiya da wakansu suna sassarfa domin suma sun gaji dokin haizar ne ka wai bai gaji ba saboda shi ba doki bane na gaskiya, dokine na sihiri. A duk sa'adda daya daga cikin dakarun yayi yun kurin tsaya wa don ya huta kodan ya nemi ruwan sha sai haizar ya da ka masa tsawa ya shiga taitayinsa, idan kwa yaki bin umarni nan take haizar zai zare takobi yasare kansa nan take bisa dole suka hakura suka hakura suka ci gaba da tafiyar a hankan bayan kwana daya ne dakarun suka rinka yanke jiki suna fadowa daga kan dawakansu matattu saboda tsananin yunwa da kishirwa sakamakon basu taho da isasshen gazuri ba masu tsananin juriya da taurinri ai ne suka kai kwana na uku amma suma alfijir na ketowa suka fadi kasa matattu ya rage saura sarki haizar shi kadai bisa dokinsa shi kansa in badon yana tsafiba ya sami ruwansha da tuni ya mutu saboda azababben zafi ranar da ake yi ga shi dazuzzukan da suke ratsawa gabadayan su saharane ko bishiya daya mutum ba zai gani ba. Lokacin da rana ta take ne haizar hango su hukairu a can gabansa tazarar da bata wuce taku dari biyar ba tsakaninsu sun doshi kofar birnins misra koda ganin haka sai haizar ya zare takofinsa yasa karwa dokin sihirinsa linzami ya zabureshi cikin masifaffen gudu. Su hukairu na cikin tafiya sai suka jiyo sukukuwar doki a bayansu. A firgice suka juyo hango wanda ke kokarin kawo musu hari cikin hanza hukairu yazare takobinsa ya tsaida rakuminsa sannan ya dubi humaira ya ce maza ki ruga bakin kofar binin misra ni kuwa zantsaya na tari wannan mahayi da ya durfafomu. Ba wanibane.face sarkin yaki haizar lallai sarki daksur ne yaturoshi ya hallakani. Koda jin wannan batu sai humai tafa she da kuka ta ce ni kam bazan tafiba na barka sai dai mutafi tare. Cikin tsananin fushi hukairu ya dakawa ya dakawa humaira tsawa ya ce idan ban tsaya ba na tareshi zai cimmanane ya hallakamu gaba daya har jaririyar dake goye a bayanki. Fatana shine ke da jaririya kutsira da rayuwarku ai ni nagama cika burina kunda har na kawo kunan bakin birninmu da na misra. " Koda jin wannan batu sai humaira ta zaburi rakuminta da gudu tanufi bakin kofar birnin misra, a wannan lokacin baifi taku arba'in ba haizar ya iso gaban hukairu Hukairu ya juya yayiwa Humaira kallon kar she cikin guntun murmushi, a lokacin da kalla ta cika idanunsa. Wai gawar da zaiyi haka sai yaga sarkin yaki haizar dab da shi har ya kawo masa wawan sara da nufin ya sare masa kai. Cikin zafin nama hukairu ya sunkuya ta kobin haizar ta sari iska shima ya zare takobinsa suka fara a zababben yaki. Nanfa suka fara kai wa juna sara da suka cikin tsananin zafinnama, juriya da bajimta ya zamana cewa dayansu ya kasa cutar da dayan al'amarin da ya matukar baiwa sarkin yaki zaihar mamaki kenan domin bai taba sanin cewa HUkairu jarumine haka ba.
Lokacin da ake wannan mugun artabu
tsakanin Hukairu da Zaihar tuni humaira
ta isa bakin kofar birnin misra amma sai
ta ja linzamin rakumin ta ta tsaya cak ta
kasa shiga birnin ta juyo cikin tashin hankali tana kallon gumurzun da akeyi
tsakanin mijinta da sadauki zaihar.
Lokacin da sadauki zaihar yaga wankin
hula zai kai shi dare sai ya fusata ya fara
amfani da karfin sihiri domin ya hallaka
hukairu amma sai ya ga ashe shima hukairu ba kyalle bane abangaren tsafi
domin karfi ya zo daya. Haizar yaja da
baya yaduru daga kan dokinsa ya tsaya
cak a waje daya yana tunanin dabarar da
ya kamata yayi. Koda ganin haka sai
shima hukairu ya duro daga kan rakuminsa ya gyara tsayuwa yana mai
fuskan tarsa sannan ya kyalkyale da
dariya yanuna haizar da dan ya tsa ya ce
"ya kai wannan tsohon azzalumi ba wan
azzalumai ka sani burin mai gidanka
bazai cikaba a kan iyalina domin sun tsira daga sharrinkku a yanzu tunda sun haye
iyakar kasarku. Ko a yanzu ka kashe ni
bani da na damar komai. Yayin da haizar
yaji wannan batu sai shima ya kyalkyale
da dariya sannan yace "ai kuwa yanzu
zan kasheka sannan nabi iyalinka har bakin kofar birnin misra suma na
hallakasu tun dadai sun kasa shiga cikin
birnin sun tsaya suna kallo domin suga
irin mutuwar dazakayi. "
Koda jin wannan batu sai hukairu yajuya
da sauri domin ya dubi bakin kofar birnin misra kafin ya juyo da kansa tuni Haizar
ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da
tsini ya wurga masa take wukar ta cake
atsakiyar kirjinsa ya dur kushe bisa
guiwowinsa koda humaira ta hango
abinda ya faru da sai ta tsandara uban ihu al'amarin da ya janyo hankalin masu
gadin kofar birnin misra kenan suka rugo
waje da gudu rike da makaman yaki suda
yawa. Yayin da sarkin yaki ya hango fito
war wadannan mayaka sai ya juyo da
sauri ya ruga izuwa kan dokinsa na sihiri ya zabure shi da gudu yanufi baya. Ita
kuwa Humaira sai ta diro kasa daga kan
ra kuminta ta falfala da gudun tsiya tana
kuka izuwa inda mijinta yake durkushe.
Koda zuwanta gabansa sai ta tabashi sai
taji ya bingire kasa ko motsi baiyiba alamar cewa yamutu ba shi da rai nan fa
ta rungume gawarsa tasake fashewa da
matsanancin kuka. Tana cikin wannan
haline dakarun misra suka zo gareta suka
banbareta daga jikin gawar da karfin
tsiya suka tafi da ita izuwa cikin birnin misra tana ta iface iface da koke koke
tamkar sabuwar mahaukaciya. Wannan
shine abin da ya faru ga Humaira matar
Hukairu bayan srkin yaki ya riskesu ya
kashe hukairu, ita da jaririyar sun tsira
A can birnin kisra kuwa lokacin da hakimi barzuk ya
koma wannan gida nasa inda ya ajiye matarsa nuzaira
sai ya shaida mata duk wadannan dokoki wadanda
sarki daksur ya shimfida masa a kan jaririyar data
haifa ko da jin wadannan dokoki sai ta cika da
tsananin mamaki ta dubeshi tace to wai shin laifin me
mukayi harda sarki zai kafawa yarmu irin wadannan
dokoki masu tsauri dayawa haka?” Koda jin wannan
tambaya sai barzuk ya tumbune fuska yace ” ni kaina
bansan daliliba amma babu mamaki akwai babbar
hujja data janyo mana hakan saboda haka indai kIna
son mu tsira rayuwarmu da mutuncinmu lallai
kikiyaye wadannan dokoki ” daga wannan rana kowa
nuzaira tacigaba da renon jaririyarta da ranar suna
tazo sai aka radawa jaririya suna yazila tunda nuzaira
ta acikin wannan gida na mijinta acikin birnin kisra
batata bin hanyar gidan sarauta ba bare ma taga sarki
da idanunta bare kuma jairiyar datake raino. Tafiya
sannu sannu kwana nesa darare na wucewa kwanaki
na shudewa sai aka wayi gari yarinya yazila ta cika
shekara bakwai a duniya nan da yazila tazama
sananniya a birnin kisra saboda kasancewarta tataso
da tsananin kyau dakuma jarumantaka domin tun a
sannan tana iya daga kato komai girmansa ta
rankwalashi da kasa har sai datakai cewa ana shirya
mata gasar kokawa da mazaje majiya karfi tana zama
zakarar gasar daga nan kuma sai lamari nata kara
samun cigaba domin ta fara koyon sarrafa
takofi`mashi`kwarida baka. Duk mutumin daya fara
koya mata amfanida kayan yaki sai yaga tafi kwarewa
acikin kwanaki uku kacal. Tun da yazila ta taso taga
wata farar laya a wuyanta bata son abin da zai rabata
da layarba dare da rana har kwanciyar barci kuwa. A
takaice dai batata cire layarba kuma tana iya tuno
lokacin da mahaifiyarta hakimi barzuk ya samata layar
sa adda batafi shekara biyarba aduniya. Koda wasa
yazila batata bin hanyar gidan sarki ba kuma kojitayi
sarki zai shigo cikin gari tobazatataba fita daga cikin
gidan domin a rayuwarta babu data tsana tagani ko
taji zancensa face sarki. Abinda batasaniba shine.
Wannan laya da aka rataya mata awuya itace sanadin
dataji batason taga sarki.
Ana nan cikin wannan hali har yazila ta cika shekara
goma sha takwas. Alokacin ne kyawunta yaruda gaba
dayan jama ar birnin kisra ya zaman cewa duk inda
mutun yaje saidai yaji ana labarinta. Afagen jaruman
taka kuwa al amarin maya wuce tunanin mai tunani
domin duk sa adda aka fita yaki da mutanen birnin
misra tana ya musu mummunar barna wata jaruma
guda daya takeci mata tuwo akwarya wadda itace
sarkin yakin mutanen birnin misra a wani lokaci ita
dai yazila taji ana yiwa jarumar kirari da basadaukiya
dabira babban abin takaici a wajen yazila shine
bata taba ganin fuskar wannan abokiyar gaba tata ba
domin duk sa adda zata fito yaki tana rufe fuskarta ne
da hular karfe. Akalla yazila da dabira sun fafata
kazamin yaki kamar sau hudu amma duk sa adda suka
hadu.kare jini biri jini sukeyi. Koda rauni suka yiwa
juna sai kaga raunin yazo adadi daya baya gotawa
sukansu suna matukar mamakin wannan al amari
babu irin kokarin da yazila batayi ba don ganin ta cire
hular karfen datake dabira taga fuskarta amma abu ya
gagara.
Akwai.wata rana da yazila ta tambayi bokanta wanda
ake kira mushrid bin affan tace dashi yakai abin
dogarona yaza ayina sami nasara akan abokiyar gabata
basadaukiya dabira na kai kasa kuma har na cire
hular karfen dake kanta naga fuskarta ?”
Koda jin wannan tambaya sai boka mushrid ya
kyalkyale da dariya sannan yace ” idan har kina son ki
sami wannan nasara sai dai ki cire wannan laya dake
wuyanki kije har cikin fadar sarki daksur ku yi arba da
juna in dai kikayi haka sai kin nasara akan jaruma
dabira har kiyi mata rauni sama da adadin wanda
zatayi miki. Kuma ki kaita kasa ki cire hular karfen
dake kanta kiga fuskarta amma ki sani cewa ranar da
wannan abu ya faru zaki shiga tashin hankali irin wanda baki tabaga
shigarsa ba”
Koda jin wannan babu sai jaruma yazila tasa hannunta
ta kama wannan farar laya dake wuyanta da nufin ta
cireta amma sai ta ji kamar an soka mata allura guda
dubu a sassan jikinta. Ba shiri ta saki layar ta kama
ihu kuma ta fadi kasa a matukar galabaice tana haki 
 kamar wadda aka yi yunkuri zare ruhinta. Nan ta jike sharkaf
da gumi da kyar ta dago da kanta ta dabi boka
mushrid tace ” me yasa na kasa cire wannan laya daga
wuyana kuma taya ya zan iya rabuwa da ita ?”
*WACCE AMSA BOKA MUSHRID ZAI BAIWA JARUMA
YAZILA?
*YAUSHENE JARUMA YAZILA ZATA YI ARBA DA
FUSKAR SARKI DAKSUR?
*YAYA AKAYI BASADAUKIYA DABIRA TAZAMO SARKIN
YAKIN BIRNIN MISRA?
SHIN ITAMA TA ZAMA MUSULMA CE?
*INA LABARIN MAHAIFIYARTA HUMAIRA?
*SHIN NUZAIRA DA HUMAIRA ZASU SAKE GANIN
JUNA?
MUHADU A JARUMA YAZILA NA BIYU DON
JIN CIGABAN WANNAN LABARI.

Comments

Popular posts from this blog

Farillai, Sunnoni da kuma Mustahabban Alwala

Jadawalin Fina-Finan Algaita

TARIHIN JARUMI MAHESH BABU