SABON TSARIN SIYAN DATA 200MB A NAIRA HAMSIN

SABON TSARIN SIYAN DATA 200MB A NAIRA HAMSIN Wannan tsari yana yi a kowanne irin layi na MTN, abunda kawai ake buQata shine ka saka Kati na Naira Hamsin a layinka na MTN. Bayan ka Saka Katin sai ka shiga wurin kira ka danna *131*25# sai ka tura. Bayan ka tura sai fara loading yana gamawa sai ya nuno maka rubutu da wasu zabuka guda biyu. Akwai mai alamar Lamba daya da kuma biyu. Abunda suke nufi anan shine, idan ka zabi lamba ta daya (1) suna nufin idan wa'adin Datar ya Qare to su siya maka wata da kansu indai akwai kudi a cikin layin. Ita kuma lamba ta biyu (2) suna nufin cewar baka BuQatar a siya maka kawai zaka siya da kanka. Toh sai ka zabi kowacce lamba a cikin guda biyu ka danna Send, shikenan zasu nuna maka wani rubutu kamar haka. Daga nan sai bude Datar ka ka fara amfani. Wa'adin wannan Datar shine Sati Biyu. Tambayar Balance na Data kuma *131*4#